Gwamnatin tarayyar Najeriya na duba yiwuwar sake saka dokar kulle a wasu jihohin ƙasar bisa la’akari da hauhawar masu kamuwa da cutar Korona.

Mai lura da ayyukan kwamitin fadar shugaban ƙasa kan cutar Korona Dakta Sani Aliyu ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi jiya Lahadi.
Ya ce mutane na bijirewa matakan kariya daga kamuwa da cutar wanda hakan ke nuni da yiwuwar sake saka dokar kulle a Najeriya.

Dakta Sani ya yi gargaɗi ga al’ummar Najeriya da su kasance masu bin dukkan dokokin da hukumar ta saka wajen bayar da tazara, wanke hannu, da kuma amfani da safar baki da hanci sai ƙauracewa cunkoso.

Ya ce ta haka ne kaɗai za a samu sauƙin ruɓanyar masu kamuwa da cutar da ake yi a wannan lokaci.