Gwamnatin jihar Zamfara ta kwace lasisin makarantu masu zaman kansu sama da 500.

Kwamishinan Ilimi a jihar Alhaji Abdullahi Ibrahim ne ya sanar da hakan ya ce an kwace lasisin makaranatun ne bisa ƙin cika sharuɗan da gwamnatin jihar ta saka.
Ya ce iya makarantun da suka cika sabbin sharuɗɗan da gwamnatin ta saka ne kaɗai za su ci gaba da gudanar da karatu a jihar

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta saka naira dubu talatin a matsayin kudin rijista ga masu makaranatun amma wasu suka ƙi cika sharuɗan.

A halin yanzu ma’aikatar Ilimi a jihar ta kammala dukkan shiri na ganin majalisa ta basu daman a lura da dukkanin al’amuran makaranatu masu zaman kansu a jihar kamar yadda kwamishinan ilimi na jihar ya bayyana.