Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da kama wasu ma aikatan ma aikatar ƙananan hukumomi da karkatar da tallafin Korona.

Ƴan sanda a jihar Oyo sun gurfanar da Adebiyi Azeez da Sunday Akinleye a gabar kotun majistire da ke Ibadan bisa zargin siyar da buhun suga 40 na tallafin Korona.,
ɗan sandan mai gabatar da ƙara Sunday Ogunremi ya tabbatarwa da kotu cewar mutanen sun aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Disamban shekarar da ta gabata.

Ƙimar kuɗin sigan ya kai naira 40, kuma kotun na tuhumarsu da laifin sata, da kuma cin amana.

Haka kuma an gurfanar da wanda ke siyar da kayan mai suna Kafayat Babalola wanda ya bayyanawa kotu cewar bai san sigan na tallafin Korona bane.
Mai shari’a Mista Taiwo Oladiran ya bayar da belin waɗanda ake zargi kan kudi naira dubu 20 kowanne.
Sannan an ɗage sauraron shari’ar zuwa 8 ga watan Fabrairun shekarar da muke ciki.