Rundunar yan sandan jihar Gombe ta kama wasu da ake zarginsu da aikata garkuwa da mutane da kuma wasu da ake zargi da yin fyaɗe.

An kama mutane biyu bisa zargin aikata fyaɗe da kuma wasu mutane uku da ake zargi da garkuwa da mutane.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Maikuɗi Shehu ya ce sun kama wani d ke ɗaukar nauyin mai garkuwa da mutanen.

A yayin da yake yiwa ƴan jarida bayani a helkwatar rundunar da ke Gombe, Maikuɗi Shehu ya ce maharan sun sace wani Alhaji Babayo wanda ƴan bindigan suka yi garkuwa da shi har suka nemi kuɗin fansa naira miliyan biyar.

Sai dai daga bisani bayan ƴan bindigan sun yi bacci wanda aka sace ya gudu kuma ya sanarwa da wani dagaci aka sanar da jami’an ƴan sanda kuma suka bisu har suka kamo ƴan bindigan.
Kwamishina mai kuɗi ya ce sun kama mutane uku daga cikin ƴan bindigan, sannan sun kashe guda daga cikinsu a yayin da suke musayar wuta.