Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da sace wasu yara su shida ƴan gida ɗaya a jihar.
Yaran da aka sace ƴaƴa ne ga Alhaji Sani Gyare da ke ƙauyen Kadauri na ƙaramar hukumar Maru a jihar.
Masu garkuwa da mutane sun shiga ƙauyen ne a daren jiya Juma’a sannan suka sace yaran su shida
Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar SP Shehu Muhammad ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.
Ya ce bayan samun rahoton sace yaran kwamishinan yan sandan jihar Abutu Yaro ya tashi dakarun ƴan sanda don ganin an ceto yaran.
Jihar zamfara na daga cikin jihohin gaba-gaba da yan bindiga ke garkuwa da mutane har su karɓi kuɗin fansa.