Wata kotun majistire a jihar Kano ta yanke hukuncin bulala 12 kowanne ga matasa biyu da aka samesu da laifin satar waya.

Jabir Idris mazaunin Jakara da Salisu Hamisu mazaunin Ɗandinshe an kama su da laifin satar waya a wurare daban daban.

Alƙalin kotun Farouk Ibrahim ya yanke hukuncin ne bayan matasan sun nemi afuwar kotun a bisa laifin da suka aikata.

ɗan sanda mai gabatar da ƙara Lamiɗo Soron Ɗinki ya shaidawa kotu cewar mutane biyun da aka satarwa wayar sun kai ƙorafinsu ne zuwa caji ofis ɗin ƴan sanda da ke Fagge.

Ƴan sanda sun kamo waɗanda ake zargi kuma suka sami wayoyin da aka sace.

Sai dai laifin da aka samesu da shi ya saɓa da sashe na 286 da sashe na 308 na kundin doka.

Kuma a bisa dalilin ne suka gurfanar da su a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: