Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce a cikin shekarar da muke ciki ta 2021 za a kawo ƙarshen ƙungiyar Boko Haram a faɗin ƙasa baki ɗaya.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a yayin da ya halarci sallar Juma’a tare da tunawa da sojojin da suka rasa rayukansu.

Ya ce wannan shekarar ta aiki ce kuma za a kammala dukkan abin da aka saka a gaba.

Muhammadu Buhari ya jinjinawa sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa kuma tarihi ba zai taɓa mantawa da sub a.

Sannan ya buƙaci sojojin da suke bakin daga da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da nasarar da aka saka a gaba.

A ƙarshe ya buƙaci addu’ar ƴan Najeriya don ganin an sami nasarar murƙushe dukkan ayyukan ta;addanci a fadin ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: