Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya ce babu lokacin da suka tsayar na kammala sabuwar waƙar da za a yi don bayyana ayyukan Buhari.

Talakawa masoya Buhari ne suka tura kuɗin kamar yadda ya buƙaci kowa ya tura naira dubu guda.

Sai dai mawaƙin ya ƙi bayyana adadin kuɗin da aka tara masa. Kamar yadda ya ce bai yi alƙawari zai bayyana adadin kuɗin ba.

Bayan wallafa labarin batun sabuwar waƙar da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya yi alkawarin yi tsawon watanni huɗu, daga bisani ya magantu a kan lamarin.

A yayin tattaaunawarsa da Mujallar Mattashiya ta wayar tarho, Rarara ya ce rikicin Endsard ne ya sa suka dakatar da aikin amma suna nan suna ci gaba da shirye-shirye don ganin an ci gaba da aikin wakar.

Rarara ya ce masoyan Buhari ya bukaci su tara kuɗi kuma sun biya kuɗin waƙar. Za a bi dukkan lungu da daƙo don ganin an ɗakko ayyukan shugaban ƙasa don nuna su a cikin waƙar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: