Hukumar lafiya matakin farko a jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane 22 a sanadin cutar lassa.

Shugaban hukumar Dakta Rilwani Muhammad ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a jihar.

Ya ce cutar ta kama mutane 57 a cikin shekarar 2020 da ta gabata.

Wuraren da aka sami masu cutar akwai Tafawa Ɓalewa, Toro, Ganjuwa, da ƙaramar hukumar Bauchi.

Sai dai gwamnatin ta gudanar da feshin kashe kwayar cutar a gidaje da kasuwanni da sauran muhimman wurare 6,000 a jihar

An sami ɓarkewar cutar a shekarar 2019 zuwa 2020 din da suka gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: