Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Gobara Ta Hallaka Mutane Uku A Kano

Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku a sanadin wata gobara da ta tashi a wani gida.

Gobarar ta tashi a wani gida da ke unguwar rijiyar zaki a ƙaramar hukumar Ungogo na jihar.

Mai Magana da yawun hukumar S’idu Muhammad ya ce gobarar ta tashi da misalin ƙarfe uku na dare.

Wani mai suna Mallam Salisu Muhammad ne ya sanar da su lamarin kuma tuni suk atashi jami’ansu don halartar wajen.

Ya ƙara da cewa hukumar ta sami fito da mutane uku Hauwa Musa Salamatu Musa da kuma Mubarak Musa, wanda likitoci a asibitin Murtala suka tabbatar sun rasu.

Sai dai har yanzu ba a gano sanadin tashin gobarar ba, kamar yadda y ace hukumar na ci gaba da bincike a kan lamarin.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: