Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci ma’aikatu masu zaman kansu da su samar da aikin yi ga matasa don rage yawan marasa aikin yi a ƙasar.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a yayin taron tsawaita shirin bata tallafi ƙarƙashin tsarin ESPWP wanda gwamnatin tarayya ta samar don rage raɗaɗin Korona a Abakiliki na jihar Ebonyi

Ya ce gwamnatinsa na yin duk mai yuwuwa wajen samar da aikin yi don rage yawan masu zaman kashe wando amma sai ma’aikatu masu zaman kansu sun tallafa.

Ya ce tsarin samar da aikin yin a tallafawa matasa a gwamnatinsa, zai taimaka wajen samarwa matasa hanyar dogaro da kansu.

Tsarin tallafin dai zai samarwa matasa dubu guda a kowacce ƙaramar hukuma ta Ebonyi su sami naira dubu ashirin duk wata har tsawon watanni uku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: