Babbar kotun ɗaukaka ƙara a jihar Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani mai suna Sunday Jimoh bayan an same shi da aikata mummunan laifi.

Wata kotu ce ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan gyaran hali tun a ranar 30 ga watan Disamban shekarar 2017 kuma ya ƙi aminta da hukuncin wanda ya ɗaukaka ƙara zuwa babbar kotun don ɗaukaka ƙara.
Alƙalin kotun ya rushe hukuncin kotun farko wanda ya yanke hukunci rataya ga Sunday Jimoh maimakon ɗaurin rai da rai.

An sami Sunday Jimoh da aikata ta’addanci ne a Omuo Ekiti na jihar.
