Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

An Haramta Zuwa Ofisoshin Gwamnati Ba Tare Da Fes Mas Ba

Gwamnatin jihar Edo ta jaddada aniyarta na haramta shiga ofisoshin gwamnatin ga ma’aikata ta masu ziyartar ofisoshin.

A cikin sanarwar da shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Anthony Okungbowa ya fitar, sanarwar ta ce babu wani ma’aikaci da zia shiga ofishin gwamnati ba tare da ya saka safar baki da hanci ba.

Sanarwar ta ce ba iya ma’aikata ba, hatta masu ziyartar ofisoshin ba za a basu damar shiga kowanne ofishin gwamnati a jihar ba har sai sun saka safar baki da hanci.

Wannan dai wani mataki ne da gwamnatin ta ɗauka na ganin an toshe hanyoyin yaduwar cutar Korona wadda ta sake zagayowa a karo na biyu.

Tuni suka ba da umarnin manyan shugabanni a ofisoshin gwamnatin jihar na ɓangare daban daban na ganin sun saka ido wajen tabbatar da dokar.

Mista Anthony ya buƙaci ma’aiakatan da su kasance masu bin dokar tare da bawa gwamnatin hadin kai don ganin an cimma manufar da aka saka a gaba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: