Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Katsina – An Gurfanar Da Masu Garkuwa Da Mutane A Gaban Kotu

Ƴan sanda a Katsina sun gurfanar da masu garkuwa da mutane su biyu a gaban kotu bayan an same su da kai hari a Katsina.

Babbar kotun majistire da Katsina ce ta ba da umarnin kai mutanen biyu Sa’adu Haruna da Musa Ibrahim zuwa gidan gyaran hali tsawon watanni uku.

An same su ne da hannu wajen kitsa wani hari da aka kai ƙauyensu Dantarkari da ke ƙaramar hukumar Ɗandume a jihar.

An kai harin ne a ranar 25 ga watan Disamban shekarar da ta gabata kuma aka kashe mutane uku tare da sace mutane da dama.

Bayan kai harin ne kuma jami’an tysaro suka shiga ƙauyen tare da fara gudanar da bincike a kai, kuma binciken ƴan sanda ya nuna cewar mutane biyun da aka kama na da hannu wajen kitsa harin da aka kai.

Jiya Talata kotun ta bayar da umarnin kai mutanen biyu zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar 1 ga watan Afrilun shekarar da muke ciki don ci gaba da shari’ar.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: