Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Mutuwar Mutane 25 – Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Ƙungiyar Asiri Su 11

Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta tabbatar da kama mutane 11 ƴan  ƙungiyar Asiri bayan an sameshi da laifin kashe mutane 25 a jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Edward Ajogun ne ya yi holen masu laifin a jihar wanda ya sha alwashin ci gaba da yaƙi da ƴan ƙungiyar a fadin jihar.

Ya ce mutane 11 da ake zargi na da hannu a kisan wasu mutane 25 da aka yi a yankin Ijebu Ode na jihar Ogun.

Ya ƙara da cewa mutanen da aka kama an same su da laifin fashi da makamai,. Da sauaran laifukan ta’addanci baya ga samun makamai daga wajen su.

A yankin kudancin Najeriya dai ana ci gaba da samun mutane ƴan ƙungiyar asiri da ke aikata fashi da makami da sauran munanann laifukan ta’addanci.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: