Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Kano KANSIEC ta ce ba za ta yi amfani da naurar tantancewa ta card reader a zaɓen ƙananan hukumomi da ke gabatowa ba.

Shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana hakan a yayin taron ƙarawa juna sani wanda aka shirya dangane da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a jihar Knao.

Ya ce ba za su iya siyan na’urar ba saboda tana da tsada kuma ba su da kudin da za su mallake ta.

Farfesa Sheka ya ce za a fara zaɓen ne daga ƙarfe takwas na safe zuwa ƙarfe uku na yamma kuma baturen zaɓe za su kammala kai sakamako zuwa ƙarfe shida.

Ya ƙara da cewa an tanadi jami’an tsaro waɗanda za sub a da gudunawa wajen tabbatar da tsaro a yayin zaɓen.

Sannan dukkan kayan zaɓe sun kammala za su fara raba su a ranar juma’a mai zuwa.

Jam’iyyu 18 ne za su shiga zaɓen da za a yi a ranar Asabar 16 ga watan Janairun da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: