Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ƴan Sanda A Katsina Sun Cafke Aljanun Boge

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun tabbatar da kama wasu matasa biyu da suke damfarar mutane a waya da sunan aljanu ne.

Matasan biyu Kabiru Bashir da Sadiƙ Ashiru ƴan ƙaramar hukumar Dala ne a Kano kuma suna basaja da sunan su aljanu ne suna damfarar mutane daban daban a jihar Katsina.

An kamasu a ranar Juma’a 8 ga watan Janirun da muke ciki.

Mai Magana da yawun ƴan sanda a jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da cewar an kama matasan kuma sun amsa laifinsu.

Ya ce sun sami ƙorafi daga wata Rabi’atu Garba da suka so su damfare ta.

Cikin wadanda aka kama an samesu ne da katin shaidar aikin hukumar tsaron fararen hula na, wayoyin hannu, mota wayoyin hannu guda biyu da tsabar kuɗi naira dubu 126

Gambo Isah ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike a kan matasan sannan su gurfanar da su a gaban kotu don girbar abinda suka shuka.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: