Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta gina katafaren gidan gyaran hali na zamani wato kurkuku a yankuna shida na ƙasar.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a yayin da ya ziyarci aikin da ake gudanarwa a gidan gyaran hali a jihar Kano.
Ya ce tsari ne da shugaban ƙasa Buhari ya ƙudirin aniyar yi don ganin an gyara tsarin gidan gyaran hali a sassan ƙasar.

A yayin da yake jawabi shugaban hukumar gidajen gyaran hali a Najeriya Ahmad Jafaru ya ce gidan gyaran halin da ake ginawa zai na ɗauke da ɗakunan kwana, makarantu, wuraren koyon sana’a sai wuraren ibada da sauransu.

Ana gudanar da aikin ginin sabon gidan gyaran hali na zamani a unguwar Janguza da ke Kano.