Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun hallaka mutane goma a garin Janbako da ke ƙaramar hukumar Maradun daa jihar Zamfara.

Maharan sun shiga ƙauyen ne ɗauke da makamai a kan Babura, a safiyar jiya Lahadi, sai dai jami’an sa kai na Bijilanti sun yi ƙoƙarin  daƙile harin.

Bayan mutane 10 da aka kashe akwai wasu mutane huɗu da suka samu raunin harbi.

Yayin da Mujallar Matashiya ta tuntuɓi mai Magana da yawun ƴan sanda a Zamafara Muhammad Shehu bai samu damar ɗaga wayar mu ba har zuwa lokacin da muke kammala muku wannan labari.

Ko da a jihar Naija ma sai da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 17 a ranar Asabar  ɗin da ta gabata.

Harin ƴan bindiga na daɗa ta’azzara a yankin jihohin arewacin ƙasar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: