Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci sarakuna biyar na jihar da su sa ido wajen ganin an magance hanyoyin yaduwar cutar Korona a karo na biyu.

A yayin wani zama da masu ruwa da tsaki a jihar Kano wanda ya gudana a yau, ciki har da sarakuna biyar na masarautar Kano, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci sarakuna su haɗa kai da hakimai da dagatai da masu unguwanni da malamai wajen ganin an shawo kan annobar.

A wannan karon dai cutar ta ruɓanya yaɗuwa a cikin al’umma la’akari da ɓullarta a farko, kamar yadda mai bibiyar harkokin kwamitin cutar na gwamnatin Kano Dakta Sabitu Shanono ya bayyana.

Ya ce baya ga mutanen da suke kamuwa da cutar a jihar Kano, adadin waɗanda cutar ta hallaka ma ya ƙaru saɓanin lokacin zuwanta na farko.

Gwamnan y ace za a zauna da shugabanni a mataki daban daban, tun daga kasuwanni, makarantu, ƙungiyoyi da malamai don ganin an samu kyakkyawan haɗin kai na magance cutar a jihar Kano.

Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya bayyana a sanarwar da ya fitar cewa,Sarkin Kano kuma shugaban majalisar sarakunan Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya tabbatarwa da gwamnatin cewar, za su yi duk mai yuwuwa wajen ganin an samar da haɗin kai na bin hanyoyin da ya kamata don daƙile yaɗuwar cutar a faɗin jihar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: