Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce gwamnatinsa za ta tallafawa ƴan kasuwar jihar waɗanda iftila’in gobara ya shafa a jiya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ya halarci babbar kasuwar wadda gobara ta laƙume dukiya mai tarin yawa.
Gobarar ta tashi ne tuna safiyar jiya Talata, sai dai ba a samu damar kashe ta da wuri ba lamarin da ya sa ta laƙume dukiya maiyawa.

Ma’aikatan hukumar kashe gobara sun isa wajen tare da ƙoƙarin kashe ta, sai dai ba su samu damar yin hakan a kan lokaci ba.

Har yanzu ba a samu tabbacin dalilin tashin gobarar ba, sai dai an ce gobarar ta fara ne daga ɓangaren ƴan roba da ke kasuwar.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal y ace zai yi duk mai yuwuwa don ganin an gyara kasuwar domin jama’a su ci gaba da gudanar da kasuwanci a cikinta.
