Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarwa ya buƙaci shugaba Buhari ya sake nazari kan batun ware kuɗaɗe don yaƙar Korona.

Bafarawa ya bayyana hakan ne jiya a Abja, ya ce al’ummar Najeriya sun fi buƙatar a magance matsalar tsaro sama da cutar Korona.

“Al’ummar Arewa sun fibuƙatar a magance musu matsalar tsaro ba Korona ba” Inji Bafarawa.

Ya ce mutanen da suke mutuwa a Najeriya a sanadin taɓarɓarewar tsaro sun ninka waɗanda ke mutuwa a sanadin cutar Korona.

Bafarawa ya ce kuɗaɗen da aka ware naira biliyan 400 ya kamata a karkatar da su don magance tsaro a maimakon Korona.

Gwamnatin tarayya dai ta ware naira miliyan 400 don siyo rigakafin cutar Korona wadda za ta iso nan daƙarshen watan da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: