Wasu da ake zargi ,yan bindiga ne sun sace wasu marayu su 8 a wani gidan marayu da ke babban birnin tarayya Abuja.

Bayan sce marayun da kuma wasu mutane, ƴan bindigan sun nemi kudin fansa naira miliyan 30.

Ƴan bindigan sun sace mutanen ne bayan jami’an tsaro sun janye daga gidan.

Bayan marayu takwas da aka sace sun tafi da mai gadin gidan da kuma wasu mutane uku maƙotan gidan marayun.

Ƴan bindigan sun shiga gidan ne da misalign ƙarfe ɗaya na daren Asabar wayewar jiya Lahadi.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar an harbi mutum guda a yayin da suka kai harin.

Harin dai ya auku ne a ƙasa da awanni 24 da janyewar jami’an tsaro daga gidan marayun.

A ɓangaren ƴan sanda kuwa sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai sun ce yara shida kaɗai aka sace skuma suna kan ƙoƙari na ganin sun kuɓutar da su.

Tuni aka bayar da umarnin rufe gidan marayun don kare rayukan al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: