Ƙungiyar tsaron yankin yarabawa Amotekun ta kama wata mata da ta siyar da jaririyarta a kan kudi naira dubu goma.

Matar ta bayyana cewar ta siyar da ƴar tata ne sakamakon mahaifin yarinyar ya gudu tun lokacin da ta bayyana masa cewar tana ɗauke da cikinta.

Tun da farko saurayin nata ya yi mata alƙawarin zai buɗe mata shago, bayan ta sanar da shi cewar tana ɗauke da ciki, ba ta sake ganinsa ba sannan ba ta san yadda za ta yi da jaririyar ba.

Seun Oladayo mai shekaru 22 a duniya ta siyar da ƴar ta ga wani Farto a jihar Ondo.

Fasto din mai suna Olawale  ya kai ƙara kan cewar sun yi yarjejeniya da ita a kan zai bawa wani likita dubu biyar bayan naira dubu goma kudin jaririyar.

Matar ta yi yunƙurin siyar da jaririyar ga wani matuƙar bai cika naira dubu biyar ba.

Jami’an tsaron sun miƙa ƙorafin ga rundunar yan sandan jihar Ondo, yayin da Mujallar Matashiya ta tuntuɓi kakakin runudnar Tie LEO Ikoro wayar sa ba ta shiga ba har lokacin da muke kawo muku wannan labara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: