Shugaban ƙasar Najeriya Muhaammadu Buhari yasallami dukkan manyan hafsoshin sojin Najeriya.

Cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasar shawara kan kafafen yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce an maye gurbinsu da sabbin hafsoshin tsaro.

Buhari ya naɗa Manjo Janar Leo Irabo a matsayin babban harsan tsaron Najeriya, sai Manjo Janar I. Attahiru a matsayin shugaban sojin ƙasa, da kuma A.Z Gambo a matayin shugaban rundunar sojin ruwa sannan Air Vice Marshal I.O Amao a matsayin shugaban rundunar sojin sama a Najeriya.

Tun tuni wasu ƴan ƙasar ke kira ga shugaban da ya sauke hafspshin tsaron ganin yadda aka gaza samun nasara a ɓangaren taɓarɓarewar tsaron ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: