Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta gurfanar da wasu mutane 22 a gaban kotu bayan an zargesu da aikata damfara a yanar gizo.

An kama mutane ne a ranar 23 ga watan da muke ciki, a Sangotedo yankin Ajah a jihar Legas.
Haka kuma hukumar ta kama wasu mutane su 16 da ake zargi da aikata damfara a wani Otel a Lekki duka a jihar Legas.

Alƙaliyar kotun sauraron laifuka na musamman Mojisola Dada ta aike da wani zuwa gidan gyaran hali har tsawon shekaru 77 bayan an sameshi da aikata damfara naira miliyan 62.

Sannan ta bayar da umarnin dawo da kuɗin da ake zargi sun damfara ga mutanen da aka damfara
Laifin damfar a jihar Legas ya saɓa da sashe na 390 (b) da sashe na 285 (9) (b).