Rundunar ƴan sanda a jihar Edo ta ce an saki kakakin hukumar shige da fice a Najeriya reshen jihar.

An sace Esene Bridged a yayin da take kan hanyarta ta zuwa coci a ranar Lahadin da ta gabata.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Chidi Nwabuzor ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a jihar.

Ya ce kakakin hukumar ta shaƙi iskar ƴanci ne jiya talata da misalign ƙarfe hudu na yamma.

Mun tuntuɓi kakakin ƴan sandan jihar ko sai da aka biya kudin fansa kafin sakinta, yayin da muka kitra wyarsa ya bayyana mana cewar yana cikin taro mu aika masa da saƙo, kum har lokacin da muke kawo muku wannan labara bai mu ji amsa daga gareshi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: