Connect with us

Labarai

Naɗa Sabon Hafsan Sojin Ruwa An Ɗora Ƙwarya A Gurbinta – Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jinjinawa shugaba Buhari bisa nada Auwal Zubair a matsayin hafsan sojin ruwa a Najeriya.

A  cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwarya fitar ya ce  Auwal Zubair ɗan jihar Kano ne da ya fito  daga yankin  ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano.

Gwamna Ganduje ya ce an ajiye kwarya a gurbinta ganin yadda hafsan sojin ruwan Auwal Zubair ya jajirce a kan aikinsa tare da samun kwarew a fanni daban daban.

Ganduje ya yabawa shugaban ƙasa Buhari a bisa naɗa sabbin hafsin sojin Najeriya wanda ya ce dukkanin waɗanda aka ɗora sun cancanta da matsayin da suke kai.

Gwamna Ganduje ya buƙaci sabbin hafsin sojin Najeriya da su saka kwarwwar aiki wajen fuskantar matsalar tsaro da Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Daga jihar Borno ma gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nuna farin cikinsa dangane da sauke manyan hafsoshin tsaro a Najeriya.

A jiya Talata shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin naɗa sabbin hafsoshin tsaro bayan ya yiwa tsofaffin ritaya.

An naɗa Janar Leo Irabo a matsayin babban hafsan tsaron Najeriya

Sai Janar I. Attahiru babban hafsan sojin ƙasa

Sannan Rear Admiral A.Z Gambo babban hafsan sojin ruwa

Sannan Air Vice-marsahal I.O Amao a matsayin babban hafsan sojin sama.

Tun tuni ake ta kiraye kiraye ga shugaban da ya sauke hafsoshin tsaron Najeriya ganin yadda al’amarin tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa.

Cikin mutanen da suke kiraye-kiraye a sauke manyan hafsoshin tsaron akwai gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum

Gwamna Zulum ya bayyana jin dadinsa cikin wata sanarwa da mai Magana da yawunsa Isah Gusau ya fitar, wanda ya tabbatar da cewar zai bayar da hadin kai ga sabbin hafsoshin tsaron da aka nada.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Zagon Kasan Da Kwankwaso Ya Yi Wa Jam’iyyar NNPP Ya Sa Ba Muyi Nasara A Kotuba- Alhaji Abbas

Published

on

Babban jigo a jam’iyyar NNPP, Alhaji Abbas Onilewura ya zargi dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso kan rasa nasarar jam’iyyar a jihar Kano.

 

A jiya Laraba 20 ga watan Satumba kotun ta yanke hukunci inda ta tsige Gwamna Abba Kabir na jam’iyyar a matsayin gwamna.

 

Kotun kuma ta tabbatar da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

 

Yayin da ya ke martani kan hukuncin, Abbas ya ce Kwankwaso ya siyar da jam’iyyar lokacin da ya ke tattaunawa da APC kan mukamin minista a Abuja.

 

Onilewura ya bayyana haka ne a yau Alhamis 21 ga watan Satumba a cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Ya ce zagon kasa da Kwankwaso ya yi wa jam’iyyar ce ya jawo rashin nasararta a hukuncin kotun da aka yanke a jiya.

 

Ya kara da cewa Wannan rashin nasara babbar asara ce a jam’iyyar mu kuma hakan ya faru ne saboda son rai na Kwankwaso wanda ya siyar da jam’iyyar.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Delta Ta Amince Da Rage Kaso 25 Na Kudin Jami’a A Jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Delta ta amince da rage kashi 25 na kudin makarantar daliban jami’a a jihar.

Wannan dai wani bangare ne na tallafin da gwamnatin za ta bai wa daliban kuma ya shafi jami’a hudu mallakin jihar.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Festus Ahon ya sanyawa hannu ranar Laraba.

Sanarwar ta ce gwamnan ya bayar da umarnin bai wa ma’aikatan jihar tallafin naira dubu goma kowanne tsawon watanni uku.

Sannan an amince da kashe naira biliyan 5.522 ga ma’aikata 50,196 a matsayinalawus da aka yi musu karin matsayi.

Sannan gwamnatin za ta kashe naira biliyan goma wajen raba buhun shinkafa 17,000 da sama da buhu masara 60,000 ga marasa karfi.

Continue Reading

Labarai

Cibiyar Kare Hakkin Yan Jaridu Ta Yi Allah-Wadai Da Cin Zarafin Yan Jarida A Kano

Published

on

Cibiyar kare hakkin yan jarida ta duniya ta yi Alla wadai da cin zarafin yan jarida da wasu yan sanda su ka yi a Kano yau Laraba.

Salim Umar na jaridar Daily Trust da Zahradden Lawal na jaridar BBC an ci zarafinsu tare da lalata layan aikinsu yayin da us ke bakin aiki.

Babban jami’in kare hakkin yan jarida na duniya Melody Akunjiyan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a yau.

Cibiyar ta ce abin takaici ne ganin yadda yan sandan su ka nuna rashin kwarewa ta hanyar cin zarafin yan jaridan yayin da su ke bakin aiki.

Cibiyar ta bukaci hukumar yan sanda ta kasa da su kula tare da kiyayewa a gaba wajen cin zarafin yan jarida musamman idan aiki ya hadasu da jami’an yan sanda.

Haka kuma cibiyar ta bukaci da aka ci gaba da bai wa yan sanda horo yadda za su dinga mu’amala da yan jarida tare da mutunta darajar dan adam.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: