Aƙalla mutane hudu ne suka mutu bayan wata sabuwar cuta ta ɓulla a jihar Sokoto.

Mutanen da suka mutu mazauna unguwa Helele ne a kwaryar birnin jihar.
Gwamna jihar Aminu Wazir Tambuwar ne ya sanar da hakan a saƙon ta’aziyyar da ya aike ga iyalan wadanda suka rasu.

Bayan mutane huɗu da suka mutu akwai wasu mutane 24 da suke asibiti waɗanda suka kamu da cutar..

Tuni gwamnatin ta kafa kwamitin kwararru don bincike a kan cutar tare da ƙoƙarin shawo kanta don kare rayukan al’umma.
Kwamitin da aka kafa zai samu jagoranci kwamishinan lafiya na jihar da kwamishinan muhalli a jihar.