Wasu ƴan bindiga sun sace mutane shida tare da kashe mutum guda a ƙauyen Avu da ke ƙaramar hukumar Lapai ta jihar Naija.

Ƴan bindigan sun shiga ƙauyen ne a ranar Talata sannan suka buɗe wuta a daga bisani kuma suka yi won gaba da mutane shida.
Wani mazaunin ƙauyen ya shaidawa Daily Trust cewar ƴan bindigan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe ɗaya na dare.

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan da suka shiga garin suna da yawa sannan suna ɗauke da makamai atare da su.

Ba mu ji ta bakin ami’an ƴan sanda a kan lamarin ba, yayin da muka kira wayar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a jihar wayarsa ba ta shiga ba har lokacin da muke kawo muku wannan labara.