Gwamnatin tarayyar Najeriya na duba yuwuwar saka dokar kulle a jihohin Kaduna, Legas Babban birninn tarayya Abuja sakamakon hauhawar samu kamuwa da Korona.

Guda cikin kwamitin da fadar shugaban ƙasa ta kafa don yaƙi da cutar Dakta Muhammad Mukhtar ne ya bayyana hakan a cikin wani shiri da aka gabatar da shi a gidan talabiji na Channels.
Ya ce gwamnatin na duba jihohin da aka fi samun masu kamuwa da cutar don saka dokar hana fita domin shawo kan annobar.

Cikin jihohin da ake samun mafi daga masu kamuwa da cutar har da jihar Plateu.

Ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar Korona a jihohi daban daban na Najeriya.
Kuma gwamnatin tarayya ta saka dokar ɗaurin watanni shida ga masu ƙin saka safar baki da hanci, duka dai don daƙile hanyoyin yaduwar cutar a tsakanin al’umma.