Rundunar ƴan sanda a jihar Osun ta ce ta sami ƙorafin wata yarinya mai shekaru 13 wadda ta zargi mahaifinta da yi mata fyaɗe.
Yarinyar ta bayyanawa jami’an ƴan sanda cewar mahaifin nata sun rabu da mahaifiyarta dalilin da ya sa suke tare da mahaifin nata a gidansa.
Ta ƙara da cewa mahaifin nata ya yi amfani da matashin kai wajen rufe mata baki sannan ya yi mata fyaɗe.
Kuma bayan ya yi mata fyaɗe ya yi mata barazana da kada ta faɗawa kowa.
Mai Magana da yawun ƴan sanda a jihar Yemisi Opalola ya ce sun duƙufa don gudanar da bincike a kan lamarin.
Kafin kaiwa ga jami’an ƴan sanda sai da aka kaiwa hukumar kare fararen hula da wata ƙungiya mai zaman kanta kuma daga bisani aka miƙa ƙorafin zuwa ga hukumar ƴan sanda a jihar.
Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Egbedore ta jihar Osun.