Matasa 26 da aka sace a jihar Taraba sun shaƙi iskar ƴanci.

A ranar asabar muka baku labarin cewar ƴan bindigan da suka kama matasan a kan hanya sun sauya musu daji daga Taraba zuwa wani daji a jihar Benue tare da neman kuɗin fansa naira miliyan 52.

Matasan su 26 guda 25 sun kuɓuta bayan jami’an soji hadin gwuiwa da ƴan sanda sun shiga dajin domin ceto su.

Ƴan sanda daga sashen daƙile masu aikata garkuwa da mutane na jihohin Taraba da Benue ne suka ka yi hadin gwiwa don ceto matasan.

Rahotanni sun nuna cewar ba a biya kudin fansa kafin kuɓutar da matasan ba.

An samu nasarar kama wasu daga cikin masu garkuwa da mutane bayan musayar wuta da aka yi tsakaninsu da jami’an tsaro.

An yi garkuwa da matasan ne a kan hanyar Wukari zuwa Takum a jihar Taraba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: