Babbar kotun jiha a Dutse jihar Jigawa ta aike da wani matashi zuwan gidan gyaran hali har tsawon rayuwarsa bayan an sameshi da aikata fyaɗe.

Mai Magana da yawun ma’aikatar shari a a jihar Zainab Baba Santali ce ta bayyana hakan a yau.

Ta ce an yanke hukuncin ne a jiya bayan an samu wani Sulaiman Ahmad mai shekaru 27 da aikata laifin fyaɗe.

Kafin yanke hukuncin sai da kotun ta bayar da dama ga wanda ake zargin ko zai iya gabatar da hujjojin da za su gamsar da kotun a kan bas hi ya aikata ba. Al’amarin da ya gaza cikawa.

Kotun ta gamsu da hujjojin ɓangaren waɗanda suke ƙara ciki har da ƙawayen wadda aka yiwa fyaɗen waɗanda suka bayyana cewar a kan idonsu ya ɗauke ta tare da kaita cikin wani kango sannan yay i mata fyaɗe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: