Majalisar dokoki a jihar Legas ta haramta dukkan ayyukan ƴan ƙungiyar matsafa jihar.

Majalisar ta yi doka ga duk wanda aka samu da aikin yan ƙungiyar har ɗaurin shekaru 21 a gidan yari, waɗanda ke ɗaukar nauyinsu kuwa ɗaurin shekaru 15.
A jiya litinin majalisar ta amince da dokar kuma sun miƙa zuwa ga gwamnan jihar domin tabbatar da ita.

A cikin dokar da aka yi a kan ƴan ƙungiyar, doka ta bayar da damar ɗaurin shekaru biyu ko sama da haka ga ɗalibai waɗanda ke skafa ƙungiyar a cikin manyan makarantu.

Ƙungiyar matsafa masu yin asiri dai na addabar kudancin ƙasar, kuma a lokuta da dama ana samunsu da aikata fashi da makami, da sauran muggan laifuka.