Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC na shirin ƙara faɗaɗa mazaɓu a jihohin ƙasar.

Shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe Festus Okoye ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Festus ya ce shirin hakan zai taimaka wajen rage cunkoso da sauƙaƙawa mutane yadda za su gudanar da zaɓe.

Sannan duba ga halin da ake ciki a Najeriya na cutar Korona, hakan zai taimaka wajen kare lafiyar al’umma a cewar Festus.

Ya ce hukumar ta taɓa yunƙurin hakan a baya amma ba a cimma matsaya a kai ba.

A sanarwar ta ce nan ba da daɗewa ba hukumar za ta zauna da masu ruwa da tsaki a ɓangare daban daban, kamar shugabannin jami’iyyu, malamai da shugabannin gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki har da gwamnatocin jihohi ganin yadda za a tsara doncimma nasarar tsarin.

An yi zaman tattaunawar ne jiya a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: