Labarai
Ɗaukar Mataki A Kan Abduljabbar Yanzu Muka Fara – Ganduje


Malamai sun ce ba bukatar muƙabala da wanda ya yi ɓatunci ga janibin Annabi Muhammad, Sallallahu Alaihi Wasallam

- Sarkin Musulmi da Wazirin Katsina sun aiko da saƙon jinjina ga Gwamna Ganduje
Matakin da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kan hana karatuttukan AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara, a Masallacinsa da ragowar wurare, Gwamna Ganduje ya ce “Wannan matakin yanzu ma mu ka fara ɗauka. Akwai abubuwan da za su biyo baya.”
A wani taro na musamman da Gwamnan ya kira dukkan ɓangarori na Malamai da kuma Limaman Masallatan Juma’a, wanda a ka yi a dakin taro na Africa House, da ke gidan gwamnati, yau Alhamis, ya ce “Da can mu na ta jin abubuwan da a ke fada sai mu ka ce a kawo mana hujja kan hakan. Mu na samun hujja sai mu ka dauki mataki kamar yadda a ka fara gani.”

Ya kara da cewa “Wannan hobbasa, ba ta gwamnati ba ce ita kadai. Ta mu ce gaba daya. Babban abin haushin ma shine, bayan karuwar faruwar irin wannan abu, sai ya zamana ma cewar abin ya na ma kara zurfi. Idan a ka yi la’akari da yadda wannan abin ya faru.”

Gwamnan ya shawarci Limaman Juma’a da cewar ya kamata Huɗubobinsu na Sallar Juma’a gobe su mayar da hankali kan wannan magana da a ke ciki.

“Ya kamata a kara nunawa al’umma munin wannan babban al’amari. Da kuma neman karin addu’o’i daga al’umma kan cewa Allah Ya sa wadannan matakan da mu ke dauka su zame mana dalilin Tsira gobe Kiyama.”
Sa’annan ya kara da cewa zai ci gaba da zama da Malaman saboda tuntubarsu kan yadda abin zai dinga tafiya. Ya kuma kara neman goyon bayan al’umma da ci gaba da yi wa jihar ta Kano addu’o’i kamar yadda a ka saba yi.
Daga cikin malaman da su ka tofa albarkacin bakinsu, sun hada da dan uwan AbdulJabbar din na jini, wato Alkali Mustapha Sheikh Nasiru Kabara, wanda ya bayar da shawarar cewar “Wannan magana ba wai magana ce ta muqabala ba. Wato ba maganar wai sai an zauna da shi ba ne. Ba abinda ya dace da shi illa a kai shi Kotun Musulunci.”
Shi ma Limamin Masallacin Al-Furqan, Dr Bashir Aliyu Umar, cewa ya yi “Wannan ai ko kadan ba magana ce ta a zauna da wannan mutumin a yi Muqabala ba ne. Ai a irin wannan mas’ala a Musulunci ba a bukatar wai a ji dalilan mutum na yin abinda ya yi.”
Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, shugaban Izalatul Bid’ah Wa’ikamatussunnah na Kano, kuma Shugaban Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano, cewa ya yi “Ba maganar wata mahawara da wanda ya zagi Annabin Tsira Sallallahu Alaihi Wasallam.”
Shi ma Shehi Shehi Maihula da Sayyadi Bashir Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari da Malamai da su ka yi magana a wajen, dukkansu sun hadu kan cewa ba bukatar zaman yin mahawara da duk mutumin da ya yi irin wadancan maganganu na batunci.
Sa’annan a jawabinsa na bude taro da takaitaccen bayani, Kwamishinan Harkokin Addini, Dr Muhammad Tahir Adam, ya bayyana irin sakonnin da su ke samu daga jama’a daban daban na yabawa da wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka.
Ya ce “Maigirma Gwamna, mu na ta samun sakonni daga gungun al’umma daban daban na goyon bayan wannan mataki da a ka fara dauka. Daga baya bayan nan mun samu sakon gaisuwa da jinjina daga Sarkin Musulmi da kuma Wazirin Katsina.”
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Alhamis, 4 ha Watan Fabrairu, 2021
cps@kanostate.gov.ng
fatimanbaba1@gmail.com
Labarai
Tsadar Karatu Na Iya Sa Rabin Ɗaliban Jami’a Su Gudu – ASUU


Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta ce kashi 50% na ɗaliban da ke karatu na iya ajiyewa saboda tsadar karatu da ake ciki a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Frafesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyana haka ya ce nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa ɗaliban da ke karatu a jami’o’in ƙasar kashi 50% daga ciki na iya ajiye karatun nasu.
A wata hira da aka yi da shugaban a gidan talabiji na Channels ranar Lahadi da daddare, ya gargaɗi ɓangaren ilimi na ƙasar da su farga a kan abinda ka iya faruwa.

Sai dai ya alaƙanta ƙara kuɗin da jami’o’i su ka yi da mafi ƙarancin albashin da ake biya na naira 30,000 a ƙasar.

Sannan ya ce akwai hatsari mai yawan gaske idan aka samu ƙarin matasa masu yawa da su ka bar makaranta.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙarawa malaman jami’a albashi da kashi 30 ga masu matsayin farfesa.
Labarai
Gobara Ta Kama A Kotun Ƙoli Ta Najeriya A Abuja


Rahotanni daga baban birnin tarayyar Najeriya Abuja na tabbatar da cewar kotun ƙoli ta kama da wuta.

Ofishin alƙalai uku aka ruwaito sun ƙone bayan tashin gobarar.
Godan jaridar Arise ya ruwaito cewar, wutar ta kama wai ɓangare na cikin kotun.

Sai dai ba a san sanadin tashin gobarar ba.

Wannan dai itace gobara da aka yi a kusa-kusa wadda ta shafi ofishin gwamnati.

Ko a watan Mayun shekarar da mu ke ciki, gobara ta kama a rundunar sojin samar Najeriya.
Yayin da a shekarar da ta gabata ta 2023 ma’aikatar kuɗi ta tarayya wani ɓangare ya kama da wuta.
Labarai
Amuruka Ta Gargaɗi Ƴan Ƙasar Mazauna Najeriya Kan Ziyartar Wasu Jihohi Har Da Kano


Ƙasar Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su kiyaye wajen ziyartar wasu jihohi da ka iya faɗawa cikin hatsari.

Sanarwar na zuwa ne bayan gudanar da wani bincike da su ka gano an samu ƙaruwar aikata manyan laifuka a jihohin.
Jihohin sun haɗa da Borno, Adamawa, Yobe, Kogi, Bauchi, Kaduna, Kano, Gombe, Bayelsa, Rivers, Enugu da jihar Bayelsa.

Sauran jihohin su ne Imo, SokOto, Zamfara, Katsina, da jihar Abia.

Ƙasar ta gargaɗi mutanenta da su kiyaye wajen ziyartar waɗannan jihohi domin su na iya faɗawa cikin tarkon masu garkuwa da mutane ko wasu miyagun laifuka.

Binciken da su ka yi sun gano cewar masu satar mutane domin neman kuɗin fansa na amfani da ƙarin mutane a wasu sassa domin cimma muradinsu.
Sannan gwamnatin Amurukan ta buƙaci ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su ƙara sanya idanu a kan dukkanin zirga-zirgarsu don gudun faɗawa hatsari.
-
Mu shaƙata8 months ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Al'ada4 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labaran ƙetare4 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Labarai4 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini3 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida
-
Labarai6 months ago
Akwai Jihohi Goma Da Zaɓen Gwamna Bai Kammala Ba A Najeriya Ko Har Da Kano?
-
Girke girke5 years ago
YADDA AKE LEMON SHINKAFA