Biyo bayan hujjojin da suka ce sun samu daga ɓangare daban-daban, rundunar ƴan sanda sun anar da cewar suna kammala tattara bayanai da za su bayyanawa kotu a kan wadda ake zargi da kashe ƴar aikin ta.

Kakakin ƴan sanda a Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewar, an samu hujjoji da suke nuni da zargin Fatima Hamza da kshe ƴar aikin ta ta hanyar azabtawa.

A cikin hujjojin da suka samu, hukumar ta ce akwai hujjar cizon mage wana suka samu daga wani likita a Kano.

Bayan ɓullar bayanin kisan ƴar aikin, hukumar ƴan sanda ta ce muzuru ne ya yi sanadiyyar mutuwarta, sai da daga baya, bayan an zurfafa bincike suka gano wasu hujjoji da ke nuni da cewar duka ne ya yi ajalin ƴar aikin.

Mutane daban-daban na bayyana ra’ayinsu dangane da mutuwar ƴar aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: