Aƙalla mutane 12 ne suka mutu yayin wani artabu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihar Plateau.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Edward Egbuka ne ya sanar da hakan wanda y ace mutanen sun mutu ne  a mabambantan rikici tsakanin manoma da maikiyaya.

Al’amarin ya faru a ƙaramar hukumar Bassa a jihar, kuma rundunar ta ce ta kama wasu mutane huɗu da take zargi da silar rikicin.

Ya ce a yayin harin an rasa dukiya mai yawa baya ga asarara rayuka na mutane 12.

Rikicin ya fara ne tun a ranar litinin ɗin da ta gabata, kuma hakan ya sa aka rasa shanu masu yawa tare da jikkata mutane da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: