A new study finds that drug prices can vary dramatically in the developing world, especially as a country moves up the economic ladder.

Hukumar lura da tuƙi a jihar Kano ta cafke wasu magunguna da ake zargoi jabu ne da wasu waɗanda wa’adinsu ya ƙare.

Ƙimar kuɗin magungunan sun kai naira miliyan 200.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Nabilisi Abubakar Ƙofar Na’isa ya fitar, ya ce an samu nasarar kama maganin ne ta hanyar bayanan sirri da hukumar ta samu.

Ya ce an kama magungunan waɗanda basu da shaidar hukumar lura da lafiyar abinci ta ƙasa NAFDAC a Nijer Street da ke unguwar sabon gari a Kano.

Hukumar ta buƙaci al’umma da su ci gaba da bayar da bayanai a kan dukkan wani abu da ba su gamsu da shi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: