Kotun majistire mai lamba takwas bayan kammala hujjoji da ƴan sanda suka yi na zargin Fatima Hamza da kashe ƴar aikin ta.

Bayan da kotuta karantowa wadda ake zargi tuhumar da ke mata ta musanta.

A zaman Kotun na yau kotun ta ƙi amincewa da bayar da belin wadda ake zargi duk da cewar lauyoyin ta sun yi roƙon hakan.

Ana zargin Fatima Hamza da kashe ƴar aikin ta ta hanyar azabtarwa da duka, tare da nuna rashin kulawa akan lafiyar ta.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin Ɗan’adam da dama ne suka ziyarci kotun don ganewa idon su yadda shari’ar za ta kaya.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan fabrairun da muke ciki don ci gaba da shari’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: