Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci taron ƙaddamar da aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa jamhuriyar Nijar.

Aikin titin jirgin ƙasa zai fara daga Kano, zuwa Jigawa, ya shiga Katsina sai ya ƙetara zuwa Nijar.

Aikin zai lashe ƙudi har dala biliyan 1.96.

An ƙaddamar da aikin a Katsina yayin da gwamnonin jihohin Kano, Katsina, da Jigawa su ka halarci taron.

Cikin waɗanda suka raka shugaban ƙasar akwai ministan sufuri Rotimi Amaechi,  ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Muhammad.

Daga jamhuriyar Nijar kuwa akwai gwamnan jihar Maraɗi Alhaji Zakari Umar da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya a Nijar.

Majalisar zartarwa a Najeriya ta amince da aikin tun a watan Satumban shekara ta 2020 da ta gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: