Jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa Aminu Sharif Momo ya ce gina masallaci ko islamiyya daidai yake da ware kuɗin zakka don shirya fina-finai.
Jarumin ya bayyana hakan ne a wani shiri da aka yi da shi mai suna ‘Barka Da Hantsi’ a Freedom Radio a Kano.
Jarumin ya ce ya kamata adinga ware wasu kuɗaɗe na zakka don shirya fin-finai a wannan lokaci.
A cewar sa da gina maallatai ko makarantu ya fi cancanta a bayar da kuɗin don shirya fina-finai saboda tasirin hakan a cikin al’umma.
Jarumin ya bayar da misali da yadda mutane suke ɓata lokaci wajen kallon fina-finai wanda ya ce idan har aka yi fim ɗin sadaƙatujjarya ne.