Gwmanan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle y ace wajibi ne a yi sulhu tsakanin ƴan bindiga da gwamnati don samar da zaman lafiya a jihohin da ake fuskantar rikicin yan bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyi daga ƴan jaridu a Jihar Adamawa.
Gwamnan ya ce zama tare da yin sulhu da ƴan bindigan shi zai bayar da damar sakin mutanen da suke tsare da su.

Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnoni su zauna da ƴan bindigan da suka buƙaci hakan domin kawo ƙarshen lamarin a jihohin da ake fuskanta.

Gwamna Matawalle ya ce babu wata hanya da za a kawo ƙarshen harin ƴan bindiga da sace mutane illa zama da su domin jin matsalolin su.
Gwamnan ya ce a matsayin san lamba ɗaya a jihar sa abin da zai yi alfahari da shin a farko shi ne ya tabbatar ya bi dukkan hanyoyi don wanzar da zaman lafiya ta yadda al’ummar sa za su samu nutsuwa.
A makon da muke ciki ne dai gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El’rufa’I ya bayyana cewar ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba.