Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da fashewar wani abu wanda har ya raunata mutane bakwai a jihar.
Jami’an tsaro sun ce wani abun fashewa ya fashe a wani gida da ke unguwar Mangworo a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.
Kwamishinan tsaro a Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce mutane bakwai daga ciki sun samu rauni.
Kwmishinan bai bayar da cikakken rahoton abin da ya fashe ba da kuma sanadiyyar fashewar.
Mutane bakwai daga cikin waɗanda suka raunata yara ne, kuma tuni aka garzaya da su asibitin koyarwa na Ahmadu Bello da ke zariya don kula da lafiyar su.