Hukumar tace fina-finai a Najeriya ta jaddada dokar tace fim ko waƙa kafin sakawa a shafin Youtube.

Muƙaddashin shugaban da ke kula da shiyyar Arewa maso yamma a Najeriya Umar G. Fage ne ya bayyanahakan a wata sanarwa.
Ya ce alhakin hukumar ne ta tace duk wani fim ko waƙa kafin a sake shi ko a ina ne.

Ko da a baya sai da mujallar Matashiya ta tattauna da shugaban hukumar na ano Mallam Isma’ila Na’abba Afakallahu wanda ya jaddada dokar a jihar Kano.

Sakamakon ɓullar hanyoyin sadarwa na zamani ya sa kasuwar kaset ta mutu lamarin da ya sa masu shirya fina-finai suka karkata zuwa shafukan sadarwar zamani musamman Youtube.
Wasu daga cikin masu shirya fina-finan sun yi amannan da dokar yayin da suke ankarar da hukumar don sassautawa domin ba a samun kuɗi a fannin.