Kwanaki huɗu da sace ɗalibai da malamai a makaranatar sakadiren kwana ta Kagara a jihar Neja.

Gwamnatin jihar ta ce tana tattaunawa da ƴan bindigan din ganin an sako ɗaliban da malamansu da ma iyalan malaman.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ibrahim Matane ne ya bayyana hakan wanda ya ce ana ci gaba da tattaunawa da su.

Alhaji Ibrahim ya musanta zargin da ake na cewar gwamnatin tarayya ta biya kuɗin fansa naira miliyan 800.

A jiya juma’a sai da sanannen malamin addininmusulunci Sheik Ahmd Gumi ya halarci inda ƴan bindigan suke domin tattaunawa da su.

Malamin ya buƙaci ƴan bindigan da su saki ɗalibai 27 namakaranatr sakadiren kwana ta kagara, da malamai uku sai mata da ƴaƴansu 12.

Sannan malamin ya buƙaci ƴan bindigan su saki fasinjojin da suka sace a kwanakin baya.

A sakamakon kama fasinjojijn da aka yi, wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda ƴan bindigan suka tsare fasinjojin wanda suka haɗa da mata da maza da kuma ƙananan yara har ma suke batun sai an biy naira miliyan 500 kafin su sake su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: