Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Bayan Ƙura Ta Lafa – Za A Buɗe Kasuwar Shasa Ta Jihar Oyo

Gwamnan jihar Oyo ya bayar da umarnin buɗe kasuwar shasa bayan da rikici ya lafa a jihar.

Gwamnan ya bayar da umarnin  buɗe kasuwar ne a yau kuma a cikin gaggawa.

Rufe kasuwar ya samo asali ne sanadin rikici tsakanin yarabawa da hausawa wanda ya yi sanadiyyar kashe hausawa da dama tare da jikkata wasu.

Sai dai a ɓangaren yan sandan jihar sun ce mutum guda aka kashe.

Wasu daga cikin gwamnaonin arewacin ƙasar nan sun halarci jihar Oyo domin ganawa da mahukuntan jihar a dangane da rikicin.

Kafin rikicin wasu daga cikin gwamnoni kudancin ƙasar nan sun yi barazanar korar Fulani makiyaya daga dazukan jihar sakamakon zargin da ake na cewar suna aikata ta’addanci.

Lamarin da fadar shugaban ƙasa ta takwa birki tare da buƙatar gwamnonin da su sauya matsayar su a kai.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: