Kotun majistire mai lamba takwas da ke zamanta a Gyaɗi-gyaɗi ta kori ƙarar wadda ake zargi da kisan ƴar aikin ta.

Kotun ta sallami wadda ake zargi mai suna Fatima Hamza a bisa rashin gabatar da hujjojin da kotu za ta. Saurari shari’ar.
Tun da farko lauyan gwamnati Muhammad Sani ya nemi a koma ga tuhumar da ake mata da farko a kan zaegin kisan ƴar aikin ta, tare da roƙon kotu ta yi hukunci a kai.

Kotu ta yi duba a bisa tuhumar tare da sallamar Fatima Hamza.

Yayin da muka zanta da Amina lauyar ƙungiyar kare haƙƙin mata ta nuna farin ciki a kan ta.
Haka zalika lauyan ƙungiyar kare haƙƙin Ɗan’adam ta duniya Barista Hussaini ya ce hukuncin da aka yanke yana bisa doka ganin cewar babu hujjar da za a duba don yin shari’a a kai.
Barita Ibrahim Cheɗi shi ya jagoranci ayarin lauyoyin da suka tsaya wa wadda ake zargi ya ce sun gamsu da hukuncin da kotu ta yi a kai.
Mai shari’a Ibrahim Khalil ya sallami wadda ake zargi bayan zaman da aka yi a kotu yau.