Bayan sakin ɗalibai da malaman da aka sace a Kagara ta jihar Neja ƴan bindiga sun sake kai hari Gidan Wamban Karaku da ƙauyen Gidan Adamu duka a Kagara.

Mutane huɗu ne suka rasa ran su.
An sace mutane 11 daga cikin su akwai mata guda bakwai.

a safiyar yau Asabar gwamnatin jihar ta bayyana cewar ta kuɓutar da ɗalibai da malaman da aka sace a Kagara ta jihar Neja.

Jihar da ke fama da harin ƴan b indiga a kwanakin nan.